1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Za a yi zaben shugaban kasa a farkon watan Yuni

Robert Adé MAB
February 29, 2024

Masu ruwa da tsaki na kasar Senegal sun kammala babban taron tattaunawa, daga cikin shawarwarin da suka bayar har da shirya zaben shugaban kasa a farkon watan Yuni.

https://p.dw.com/p/4cyjz
Macky Sall
Macky SallHoto: RTS/Reuters

 Senegal: Shirin afuwa ga fursunonin siyasa: Shirin tattaunawar ya tanadi kuma yin afuwa ga fursunonin da suka haddasa jerin zanga-zanga kin jinin gwamnati tsakanin 2021 zuwa . Amma kafin gwamnati ta yanke shawara kan shawarwarinta, masu fafutukar kare hakkin jama'a sun riga sun tashi tsaye don adawa da matakin tattaunawar. 

Senegal I Wahlen -  Macky Sall
Hoto: Ngouda Dione/File Photo/REUTERS

Babban taron tattaunawar da aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa ya bayyana karara cewar ba za a iya gudanar da zaben shugaban kasa kafin karshen wa'adin mulkin Macky Sall a ranar 2 ga Afrilu ba. Amma dai 'yan takarar shugaban kasa 16 da hadakar kungiyoyin farar hula ta Aar Sunu Election da ke nufin (Bari mu kare zabenmu) da kungiyar ‘yan kasuwa da masana'antu sun riga sun yi watsi da duk wani yunkuri da ba wa shugaban kasar Senegal damar ci gaba da mulki bayan  karshen wa'adin da dokata ta tanada. Saboda haka ne suka kaurace wa zaman taron da shugaba Macky Sall ya shirya a Diamniadio da ke kusa da Dakar.

Senegal Protest in Dakar
Hoto: John Wessels/AFP

  Djibril Gningue da ke shugabantar gamayyar kungiyoyi da ke fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci a zaben kasar Senegal, ya nunar da cewa kotun tsarin mulkin kasar ta riga ta dauki matakin da ke nuna cewa Shugaba Macky Sall ba zai iya tsawaita wa'adinsa ko shirya zaben shugaban kasa bayan karshen wa'adinsa ba."Tsayar da jadawalin zabe bayan karshen wa'adinsa da ya yi, ya saba wa hukunci da kotun tsarin mulki ta yanke. Hakan kuma ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar Senegal. Sannan wannan mataki na iya jefa Senegal cikin wani mummunan rikicin siyasa."

Shawara ta biyu da babban taron Senegal ta bayar ta shafi dokar yin afuwar bai daya ga 'yan siyasa da wadanda ke da hannu a tashe-tashen hankula da kasar ta yi fama da su a baya. Sai dai wannan mataki ya haddasa bakin ciki tsakanin 'yan uwan wadanda ke tsare, in ji Lucie Sané da ke shugabantar gamayyar kungiyoyin iyalan   fursunoninsiyasa. Ta ce a fili yake cewa azabtarwa da kashe-kashen da aka samu a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024 ba za a yi hukunci a kansu ba, alhali wadanda abin ya shafa na jiran a yi musu adalci. "Wadannan fursunonin siyasa, an kama su ne ba bisa ka'ida ba, bisa manikisar siyasa don kawar da abokin hamayya. Su yarda cewa sun zalunci wadannan mutane musamman wadannan matasa. Mun rasa yara, akwai mutanen da suka rasa wani bangare na jiki. Idan ma an tanadi yafiya, dole ne a fara fayyace wadanda ke da  alhakkin kashe-kashen. Ko ya za ta kaya dai, mu a matsayinmu na iyalan wadanda ake tsare da su, muna ganin cewa wannan kudiri na yin afuwa bai shafe mu ba.''


Senegal Demonstration in den Straßen von Dakar
Hoto: Stefan Kleinowitz/AP Photo/picture alliance

Mahalarta taron tattauna rikicin Senegal dai sun nuna bukatar kiyaye jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasa 19 da kotun tsarin mulki ta amince da su. Amma a daya hannun, sun ba da shawarar a sake duba takarar 'yan siyasa da aka yi watsi da takardunsu. Duk wadannan shawarwari za a gabatar da su a wannan Laraba a taron majalisar ministoci da Shugaba Macky Sall zai jagoranta kafin a mika su ga kotun tsarin mulkin Senegal don bayyana matsayi.