1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Shirin afuwa ga fursunonin siyasa

February 27, 2024

Shugaban Senegal ya sanar da aniyar yin afuwa ga fursunonin da aka tsare sakamakon tashe-tashen hankula da kasar ta fada kusan shekaru uku, a kokarinsa na yayyafa ruwa ga wutar rikicin da ya barke bayan dage zabe.

https://p.dw.com/p/4cvBI
Senegal: Shirin ahuwa ga fursunonin siyasa
Senegal: Shirin ahuwa ga fursunonin siyasaHoto: SEYLLOU/AFP/Getty Images

Shugaban Macky Sall ya sanar da hakan ne a daidai lokacin da ya fara taron tuntubar juna da 'yan siyasa kan jadawalin zabe, taron da 'yan takara 17 daga cikin 19 da aka tantance suka kauracewa.

Karin bayani: Senegal: Kokarin shawo kan rikicin siyasa

Shugaban mai barin gado zai mika kudirin dokar yi wa fursunonin afuwa ga majalisar ministocin kasar, kafin daga bisani a mika wa majalisar dokoki domin amincewa da shi.

Daruruwan mutane ne dai ke tsare a Senegal ciki har da madugun adawa Ousmane Sonko da kuma dan takara Bassirou Diomaye Faye da kotun tsarin mulki ta tantance, sai dai batun afuwa ga fursunonin ba shi ba ne a gaban 'yan adawan wadanda suka kafe a kan bukatar a shirya zabe kafin ranar biyu ga watan Afrilu mai zuwa.