1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mahamat Idriss Deby zai tsaya takarar shugabancin Chadi

Binta Aliyu Zurmi
March 2, 2024

Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Deby ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a zaben da ke tafe a watan Mayu.

https://p.dw.com/p/4d6if
Tschad - Anschlagsversuch
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP/Getty Images

Janar Mahamat wanda ya dare madafun iko bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2021, ya yi alkawarin mayar da kasar kan mulkin dimukradiyya a watanni 18 kafin daga baya ya dage ranar zaben.

Dage ranar gudanar da zabe a Chadi ya janyo mumunar zanga-zanga da ta hallaka mutane sama da 50.

Sanarwar na zuwa ne kwanaki bayan kisan madugun adawa Yaya Dillo a wata arangama da jami'an tsaro a birnin Ndajamena.  

Amma Kungiyar 'yan tawayen Chadi ta Front for Change and Concord da jam'iyyar adawa ta CNRD sun bayyana mutuwar Dillo a matsayin kisa don kawar da abokan hamayya.