1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hari a Chadi ya hallaka mutane da dama

Abdullahi Tanko Bala
February 28, 2024

Mutane da dama sun mutu a wani hari da aka kai kan ofishin hukumar tsaron cikin gida a kasar Chadi

https://p.dw.com/p/4czE9
Yaya Dillo tsohon dan takarar shugaban kasa a Chadi
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Wani hari da aka kai cikin dare kan ofishin hukumar tsaron cikin gida a N'Djamena babban birnin kasar Chadi ya hallaka mutane da dama a cewar gwamnati inda ta zargi wasu mutane a cikin jam'iyyun adawa.

An tura sojoji zuwa kewayen ofishin jam'iyyar adawa ta PSF kamar yadda wani dan jaridar AFP ya ruwaito  yayin da aka rufe dukkan hanyoyi da suka dangana da ofishin hukumar tsaron ta cikin gida.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce harin dai ya zo ne bayan da aka tsare wani jigo na jam'iyyar PSF da ake zargi da yunkurin kashe shugaban kotun kolin kasar ta Chadi