1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari ya jikkata dakarun MDD a Mali

Mouhamadou Awal Balarabe
May 6, 2023

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda bakwai sun jikkata a tsakiyar kasar Mali, sakamakon fashewar wata nakiya a lokacin da ayarin motocinsu ke wucewa.

https://p.dw.com/p/4QzrO
Dakarun MINUSMA da ke kiyaye zaman lafiya a MaliHoto: Sia Kambou/AFP

Cikin wani sakon da ta wallafa a shafukan sada zumunta, rundunar MINUSMA da ke tabbatar da zaman lafiya a Mali ta ce wadanda harin ya ritsa da su na samun kulawar da ta dace, ba tare da bayyana halin da suke ciki da kasashensu ba.

Wannan dai shi ne harin bam ko nakiya na shida da aka kai a shekarar 2023 a tsakiyar kasar Mali, da ke zama tungar masu ikirarin jihadi da tashe-tashen hankula, lamarin da ke haddasa zubar da jini a kasar da ke yankin Sahel.

Ita dai Minusma mai sojoji kusan 12,000, ita ce tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta fi fama da asarar rayuka mafi yawa a duniya a 'yan shekarun nan, inda membobinta 185 suka mutu a cikin shekaru 10.