1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ramadan: Kungiyoyi sun tallafi talakawan Najeriya

April 1, 2022

A jihar Zamfara mai fama da matsalar tsaro a Najeriya, an raba tallafin kayan abinci ga mabukata albarkacin zuwan watan azumi. Tsohon gwamnan jihar Abdul-aziz Yari Abubakar ya bada nau'ikan kayan abinci dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/49Ly0
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Shugaban kwamitin raba kayan azumin a Zamfara Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ya shaida wa DW cewa an bayar da tallafin ne saboda halin tsadar rayuwa da Najeriya ke ciki.

"Mai girma tsohon gwamna ya raba tireloli dari da hamsin a wannan hidima ta azumi domin ganin cewa an taimaka ma al'umma ganin tsananin rayuwa da suke ciki.‘‘ 

Alhaji Abdullahi Sani mazaunin Gusau na cikin wadanda suka samu tallafin. Ya ce babu abin da za su ce sai ‘’muce Allah ya yi masa (wanda ya kawo tallafin) sakamako da gidan Aljanna.’’ Ita kuma Salamatu Ibrahim ta ce ta ji dadin yadda ‘yan gudun hijira da marayu suka samu tallafin kayan azumin na dan siyasa Abdul-Aziz Yari.

A kudancin Najeriya ma wau kungiyoyi irinsu Orphanage and Child Care Foundation da ke unguwar Agege ta birnin Lagos sun bayar da kyaututtuka gabanin fara azumin na bana. Shugaban kungiyar Alhaji Umar Atana ya ce sun mayar da hankali wurin tallafa wa kananan yara da ke da burin zuwa makaranta.

Bildergalerie Ramadan
Hoto: Afolabi Sotunde/Reuters

‘‘Idan aka taimaka wa kananan yara suka yi karatun  addini da na boko, to muna sa ran za a ga raguwar tashin hankalin da ke faruwa a Najeriya‘‘ inji shugban kungiyar da ke tallafa wa Hausawa mazauna Lagos.

Malaman addini irin su Malam Shehu Ladan Army Malumfashi a jihar Katsina na cewa babu wani lokaci da ya fi cancanta mawadata su tallafa wa marasa karfi fiye da watan azumi. "Yanzu fa ana cikin halin kunci da talauci. Al-qur'ani ya yi magana cewa a taimaki wadanda suka tambaya da ma wadanda ba su tambaya ba" inji Ladan Army, malamin makaranta a kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani