1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rafah: Isra'ila ta nuna damuwa kan matakin Amirka

May 9, 2024

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan ya nuna damuwa kan barazanar Shugaba Joe Biden na Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ilan tallafin makamai idan ta kuskura ta shiga birnin Rafah da ke a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4fflZ
Hoto: Michael Gottschalk/picture alliance/photothek

Mr. Erdan ya ce wadannan kalamai na Shugaba Biden sun yi tsauri musamman ganin yadda shugaban ya jajirce wajen goyon bayansu tun bayan da rikici ya barke a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

Isara'ila ta yi watsi da kira-kirayen da kasashen duniya ke mata na shiga birnin na Rafah, inda tuni ta tura tankokin yaki tare da kokarin kaddamar da farmaki a kan iyaka, inda ta ce nan ne tungar karshe ta kungiyar Hamas duk da yadda wurin ke cike da Falasdinawa fararen hula.

A safiyar Alhamis din nan, rahotanni sun ce an kaddamar da wani mummunan farmaki a Rafah, hakan na zuwa ne daidai lokacin da Isra'ila ke cewa tana zafafa farmaki a arewacin Zirin Gaza domin karya lagon kungiyar Hamas.