1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya sha alwashi kakkabo jiragen yakin Ukraine

March 28, 2024

Shugaban Vladmir Putin na Rasha ya ce dakarun Moscow ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kakkabo duk wani jirgin saman yaki kirar F-16 da aka bai wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4eElq
Rasha ta ce za ta kakkabo jirgane yakin Ukraine kirar F-16
Rasha ta ce za ta kakkabo jirgane yakin Ukraine kirar F-16Hoto: Mindaugas Kulbis/AP Photo/picture alliance

Shugaba Vladmir Putin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matuka jiragen yakin kasar. Shugaba Putin ya ce, Rasha za ta harbo jirgin kamar yadda take yi wa duk wasu makamai da kasashe mambobin NATO ke tallafa wa Ukraine din da su.

karin bayani: Kawayen Ukraine za su ba ta jiragen yaki

Kasashen Beljiyam da Denmark da Norway da kuma Netherlands na daga cikin wadanda da suke yi alkawarin bai wa Ukraine din tallafi jiragen yakin na F-16, kana hadakar kasashen kawacen kungiyar tsaro ta NATO su ma suka yi alkawarin horas da matuka jiragen saman yakin Ukraine kan yadda za su yi amfani da jiragen. Sai dai shugaban ya musanta zargin shirin kasar na kaddamar da hari kan kasashe mambobin NATO.