1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Darajar Naira na kara faduwa a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2023

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa darajar kudin kasar na kara faduwa, inda a yanzu haka ake canja kowacce dalar Amurka kan Naira 1,100 a kasuwannin canjin kudin kasashen ketare na bayan fage.

https://p.dw.com/p/4XixA
Najeriya | Naira | Faduwa | Daraja | Dalar Amurka
Darajar Naira ta kara shiga halin tasku a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kwana guda bayan darajar Nairar ta fadi kasa a hukumance zuwa Naira 980 kan kowace dalar Amurka, sakamakon karancin dalar Amurkan da ake ci gaba da fuskanta a kasar. Darajar Naira da dama aka bar wa kasuwa ta yi halinta a kasuwannin bayan fagen, ta kara shiga halin tasku tun bayan dage takunkumin takaita hada-hadar kudi a kasuwanni a hukumance da gwamnatin Najeriyar ta yi.