1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin arziki na barazana ga Hajjin 'yan Najeriya

Uwais Abubakar Idris MAB
November 2, 2023

kashi 89% na kujerun aikin Hajjin bana ne aka kasa samun maniyatan da suka biya kudin ajiyarsu na Naira milyan 4.5 a Najeriya, abin da ke nuna matsanancin komabayar tattalin arziki da kasar ke fuskanta

https://p.dw.com/p/4YK1V
Miliyoyin Musulmi ne ke aikin Hajji a kowace shekara ciki har da 'yan Najeriya
Miliyoyin Musulmi ne ke aikin Hajji a kowace shekara ciki har da 'yan NajeriyaHoto: Amr Nabil/AP Photo7picture alliance

Wannan sauyi ne da za'a ce ba'a taba ganin irinsa ba a ‘yan shekarun nan a harkar aikin Hajji a Najeriya, domin guraben aikin Hajjin da ake rige-rige na sayesu har ma da kamun kafa a yanzu sun zama babu mai biya. Duk da tsawaita wa'adin biyan kudin ajiya na Naira milyan 4.5, mutane 3000 ne suka biya daga cikin kujeru 95,000 da aka kebe wa Najeriyar, kamar yadda Dr Abdullahi Rabiu Kwantagora sakataren hukumar jin dadin alhazan Najeriya ya bayyana.

Karin bayani: Zanga-zangar maniyyata aikin hajji

Dama dai bisa al'ada manoma da makiyaya ne kan gaba wajen biyan kudin aikin Hajji a Najeriya, amma kuma matsaloli na rashin tsaro sun kassaar manyan sana'o'in biyu. Sai dai Idris Ahmed Almakura da ke zama  shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Nasarawa ya ce akwai matakan da suke dauka a yanzu.

Karin bayani:Nijar: An rage kudin zuwa aikin Hajji 

Ba a barin mata a baya a filin jirgin saman Kano wajen zuwa Saudiyya don sauke farali
Ba a barin mata a baya a filin jirgin saman Kano wajen zuwa Saudiyya don sauke faraliHoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/GettyImages

Hukumar kula da aikin Jajjin Najeriya ta kara wa'adin da ta bayar na biyan kudadden ajiya da a bana sune mafi tsada da aka taba gani a tarihin aikin Hajji a kasar. Abubakar Salishu shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Adamawa na fatan a samu damar warware matsalar. 

Tun lokacin da gwamnati ta janye tallafin aikin Hajji a Najeriya ake fusknatar karuwar kudin aikin Hajji a kowace shekara.