1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Rashin nasarar MONUSCO a Kwango

Judith Raupp, Goma AH
August 14, 2023

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango na kokarin ganin an janye dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya na MDD. Sai dai kuma ta yaya za cimma haka ba tare da cutar da jama'a da kuma tattalin arziki kasar.

https://p.dw.com/p/4V8dC
Dakarun MONUSCO a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango
Dakarun MONUSCO a Jamhuriyar Dimukaradiyyar KwangoHoto: MONUSCO/Xinhua/picture alliance

Shugaba Félix Tshisekedi ya daina ba da aminci da yarda ga rundunar ta MONUSCO ta wanzar da zaman lafiya sannan da gaske yake kwarai da aniya cewar lokaci ya yi da MONUSCO za ta janye a cewar Onesphore Sematumba, wani manazarci a cibiyar bincike ta Crisis Group da ke ba birnin  Nairobi. Wanda ya ce hulda tsakanin Kwangon da MONUSCO ta yi tsami: ''Dangantaka tsakanin Monusco da gwamnatin Kongo ba ta da kyau ko kadan. Akwai rashin amincewa da juna tsakanin shugaba Tshisekedi da Monusco, akwai irin wannan tunanin a bangaren gwamnati cewa Monusco ba ta da  wani amfani, musamman a wannan lokaci na yaki da kungiyar 'yan tawaye M23.''

Duk da dakarun MONUSCO amma ana ci gaba da samun kashe-kashen rayuka

Zanga-Zangar adawa da dakarun MONUSCO a garin Goma
Zanga-Zangar adawa da dakarun MONUSCO a garin GomaHoto: Moses Sawasawa/AP/picture alliance

Dakarun na MONUSCO suna  jibge a lardunan Kivu ta Arewa, da Kudancin Kivu da kuma Ituri da ke gabashin kasar. Ko da yake Majalisar Dinkin Duniya ta kasance a Kwango fiye da shekaru ashirin, al'ummar kasar na fama da hare-haren 'yan bindiga. Wata kungiya ta masu sa ido kan kare hakkin dan Adam a Kivu Security Tracker ta yi rajista sama da mutane dubu 10,500 da aka yi garkuwa da su da kuma mutuwar mutane sama da dubu 11,600 tun daga shekara ta  2017 ya zuwa ranar 11 ga Agusta, 2023. Duk da kasancewar dakarun na MONUSCO a Kwango mayakan kungiyar 'yan tawaye ta  M23 sun mamaye yankunan arewacin Kivu da ke arewa maso gabashin kasar  nda suka katse hanyoyin sufuri zuwa babban birnin lardin Goma. Bienvenu Matumo wani dan fafutuka ya ce wani bin dakarun MONUSCO suna kusa za a kai hari amma su gaza kai dauki: ''Babu amfanin ci gaba da kasancewar rundunar da ta gaza a kusan rabin karni ba tare da ta kawo zaman lafiya ba a Kwango, su amince kawai su nade kayansu su tafi, muna goyon bayan cewar MONUSCO ta fice, ta gaza. Ana ci gaba da yanka mutane musamman a gabashin Kwango ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankula duk da cewar MONUSCO na da bayyanai dala-dala kan abin da ke faruwa.''

Dakarun MONUSCO na jin tsoron kai dauki ga wadanda ake kai wa hare-hare

Dakarun MONUSCO bayan wani harin kwantan bauna a yankin Kibumba
Dakarun MONUSCO bayan wani harin kwantan bauna a yankin KibumbaHoto: Alexis Huguet/Getty Images/AFP

Galibi farar hular kan cewar da sun sanar da jami'an rubdunar ta MONUSCO kan cewar ga wurin da ake cikin kai hari su kan ce hanya ba kyau ko suna da matsala ta abin hawa da ya lalace. Abin da Veronika Weidringer, shugabar ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, a sashen kula da hulda da jama'a, yar asilin kasar Jamus wadda ta yi  shekaru 10 a Kwango take cewar yana da wuya jama'a su fahimci cewa sojojin Majalisar Dinkin Duniya sun gaza, saboda munanan hanyoyi ko kuma lalacewar ababen hawa:"Gaskiyar magana shi ne cewar masu aikin wanzar da zaman lafiyar ba sa son wani ya mutu a cikin sahunsu Ana tura su can don aikin samar da zaman lafiya da kuma kokarin rage asarar rayuka. Amma su kan boye inda tarzoma ta taso. Abin na daure mini kai me ya sa dakarun wanzar da zaman lafiyar akasari da wani yamutsi ya taso ba su kai dauki.'' An dai yi ta samun fusata a lokuta da dama a zanga-zangar da aka kashe sojoji da fararen hula na Majalisar Dinkin Duniya saboda gazawar rundunar: MONUSCO na daukar sojoji dubu14,000 da hafsoshi da masu ba da shawara kan soji. Tare da kasafin kudin shekara na dala biliyan 1.1, MONUSCO na daya daga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD mafi tsada. Wasu kwararru dai na yin gargadi game da janyewar sojojin Majalisar Dinkin Duniya nan take, a kasar ta Kwango tun da sojojin cikin gida da 'yan sanda na Kwango ba su da isashen horo don kare al'umma dab da lokacin da ake tunkarar sabbin zabubbuka a kasar.