1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Ko ana iya rufe babin Faransanci a nahiyar Afirka?

March 20, 2024

Ranar harshen Faransanci ta duniya (20 ga watan Maris) ta gamu da cikas, ganin yadda kasashe masu amfani da shi ke maye amfani da shi da harshunansu na asali. Wannan na da nasaba ne kuwa da sabawa da kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/4dwdW
Pro-Putsch-Demo in Nigers Hauptstadt Niamey
Hoto: AFP

Ranar 20 ga watan Maris ta duk shekara rana ce da aka kebe domin kasashen masu magana da harshen Faransanci a duniya. Sai dai ranar ta bana na zuwa ne a daidai lokacin da tasirin Faransa ke kara raguwa a kasashen Afirka da ke kokarin maye gurbin harshen faransanci da suka gada daga Turawan mulkin mallaka da harsunanasu na gida.

Ruwanda da ke gabashin nahiyar ta maye gurbin harshen Faransanci da turancin Ingilishi, kazalika kasar Gabon da ke tsakiyar Afirka da kuma wasu kasashen uku da ke yammacin nahiyar da suka hada da Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar su ma suna yunkurin bankwana da harshen da suka gada daga turawan mulkin mallaka na uwar gijiyarsu Faransar. Hakan watakila na da nasaba da kyamar Fasransa da ake nunawa a wadannan kasashe wanda ya kai ga yin rabuwar 'yan bori.

Zanga-zangar adawa da Faransa a Nijar
Zanga-zangar adawa da Faransa a NijarHoto: STR/AFP/Getty Images

A baya dai Faransacin ya kasance harshen da Faransa ke amfani da shi don yada manufofinta na mulkin mallaka. Wannan ne ya sa bayan katse huldar diflomasiya da ita, wasu kasashe ke neman taka wa harshen burki.

Daga cikin mutane miliyan 300 da ke magana da harshen Faransanci a kasashe 106 na duniya, kaso mafi yawa na zaune a nahiyar Afirka, galibi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sannan kuma harshen na kara samun tagomashi daga wasu kasashe rainon Ingila ciki har da Najeriya da Ghana.

Duk da dai raguwar tasirin Faransar a Afika, wata kididdiga ta nunar da cewa harshen Faransanci na zama harshe na uku da aka fi amfani da shi a fannin kasuwanci, sannan kuma wani hasashe ya yi nuni da cewa nan zuwa shekarar 2050 Faransanci zai iya yi wa sauran harsuna zarra domin zama na biyu a duniya.