1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar da Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS

Fauziyya Dauda Abdoulaye Mamane
January 28, 2024

A wata sanarwar hadin gwiwa da aka karanta a kafar yada labarai mallakar gwamnatin Nijar, kasashen Mali da Burkina Faso da Mali sun bayyana matakin hannun riga da kungiyar Ecowas

https://p.dw.com/p/4blWH
 Assimi Goïta, Abdourahamane Tiani, Ibrahim Traoré
Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Gwamnatocin kasashe uku na yankin Sahel da ke karkashin jagorancin sojoji da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, sun sanar da ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO.

A cikin sanarwar hadin gwiwar da aka karanto a gidan talabijin na kasar Nijar, kakakin majalisar mulkin soji a Njiar, Kanar Amadou Abdrahmane ya ce, bayan shekaru 49, masu kishin Burkina Faso da Mali da Nijar na takaicin ganin cewa kungiyar ECOWAS na kaucewa manufofin wadanda suka kafata don ci-gaban yankin.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, kungiyar ta gaza taimakawa wadannan kasashen a yankin da suke fama da ta'addanci da ma rashin tsaro.