1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rundunar sojin Chadi ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga

Ramatu Garba Baba
May 17, 2023

Gwamnatin Chadi ta jinjina wa sojojin kasar bisa bajintar hallaka wasu gungun ‘yan bindiga a wani farmakin hadin gwiwa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4RWQM
Chadi na fama da matsalar tsaro
Hoto: AFP/A. Marte

Gwamnatin Chadi ta jinjina wa rundunar sojin kasar bisa bajintar da suka nuna a yayin wasu hare-hare da suka hallaka wasu gungun ‘yan bindiga a wani farmakin hadin gwiwa da ta ce,  ba a taba ganin irinsa ba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ministan tsaron kasar Daoud Yaya Ibrahim ya fada ma kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, sojojin sun yi nasarar kama wasu talatin daga cikin 'yan bindigan bayan da suka lalata sansaninsu. Kasashen Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun jima suna fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da rikicin kabilanci a kan iyakokin kasashen.