1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Barazana ga daular sarakuna a kasashen Larabawa

Abdul-raheem Hassan
November 13, 2023

Zanga zangar goyon bayan Falasdinawa na yin matashiya ga zanga zangar dimukuradiyya a wasu kasashen Larabawa a 2011. A yanzu shugabannin kama karya a yankin na fargabar rikicin Gaza na barazana ga mulkinsu a cikin gida

https://p.dw.com/p/4YlEP
Ägypten Kairo | Cairo Summit for Peace
Hoto: The Egyptian Presidency/REUTERS

A karshen watan Oktoba, 'yan Masar sun samu damar gudanar da zanga-zanga, abinda suka dade suna nema. Duk da cewa gwamnatin mulkin kama karya ta Shugaba Abdel Fattah el-Sissi na adawa da gangamin jama'a a fadin kasar, amma a wannan karon, ta amince da zanga-zangar goyon bayan Falasdinu bisa tsauraran sharudda. Amma duk da haka, wasu masu zanga-zangar da suka taru a dandalin Tahrir cibiyar juyin juya halin kasar a shekarar 2011 da ya hambarar da tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak na kira da a samar da canji da walwala da adalci a cikin kasar. 'Yan sandan sun kame sama da mutane 100. 

Hossam el-Hamalawy, masani mai bincike kuma mai fafutuka mazaunin Jamus, na cewa

Zanga zangar goyon bayan Falasdinawa a Berlin
Hoto: Christophe Gateau/dpa/picture alliance

"Yayin da wannan yaƙin ke ci gaba da jan hankali, hakan na iya faruwa. Ba ina ba da shawarar a nan cewa muna gab da fuskantar abinda aka gani a 2011 ba. Domin akwai bambanci sosai tsakanin halin da masu adawa da juna ke ciki a yanzu da 2011, lokacin da juyin juya halin ya barke shekaru goma ko fiye da haka. Akwai kungiyoyi a kasa wadanda za su yi gangami da kuma ci gaba da gudanar da gangamin. To amma abin da al Sisi yake yi tun a shekarar 2013 shi ne ya na ruguzawa da lalata duk wata kungiya da ba ta da alaka da 'yan adawa kadai ba, a'a har ma ta kasance mai cin gashin kanta daga jihar."

Gwamnatin Masar ba ita ce kawai gwamnati a yankin da ke tsoron cewa batun Falasdinu wanda yawancin talakawan da ke zaune a Gabas ta Tsakiya ke matukar tausayawa na iya yin barazana ga matsayin siyasa ba, Ita ma gwamnatin Bahrain da ta sahale wa zanga-zangar tausayawa Falasdinu bayan haramta zanga-zanga tun shekara ta 2011, an ga wasu na nuna Sarkin Bahrain rike da hannun Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyah, matakin ya kai ga tarwatsa zanga-zangar da karfin kaki. Joost Hiltermann, wani mai sharhi kan siyasar Gabas ta tsakiya ne.

Zanga zangar goyon bayan Falasdinawa
Hoto: Wolfgang Maria Weber/IMAGO

"Yadda shugabannin Larabawa ke ganin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kan tituna, sun kasance a koyaushe suna barin waɗannan a matsayin hanyar da mutane za su huce fushinsu, amma takobi mai kaifi biyu ne mai yiwuwa. Kuma cewa idan wasu yanayi suka yi muni a cikin kasa, waɗannan 'yan zanga-zangar na iya komawa gida su zama masu suka ga gwamnatin da ke mulki. Don haka dole ne su yi taka tsantsan game da inda ba kawai ba da izinin wasu zanga-zangar ba, amma kuma suna sarrafa su sosai."

A Tunisiya ma an gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, inda Shugaban kasar Kais Saied ke amfani da jinkai da yake nunawa kan halin da Faladsinawan ke ciki don samun goyon baya da kuma inganta siyasarsa na cikin gida.

"Falasdinawa a koyaushe sun kasance abin siyasa ga matasan Masar a kullum. Bayan haka, tashin hankalin na 2011 a Masar a zahiri shi ne kololuwar tsarin tattara rashin amincewa da ya fara da intifada na biyu na Falasdinu shekaru goma da suka gabata. Da yawa daga cikin masu fafutukar siyasar Masar, walau wadanda suka jagoranci juyin juya hali ko kuma wadanda suka gabata, kofarsu ta shiga siyasa, ita ce manufar Falasdinu."

Halin da ake ciki ya fallasa raunin gwamnatocin kasashen Larabawa, ciki har da Masar, da gazawarsu wajen yin tasiri a kan abin da ke faruwa, don kare Falasdinawa ko kuma na shawo kan Isra'ila ta amince da tayin tsagaita wuta.