1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta katse Internet

Abdul-raheem Hassan
February 13, 2024

Gwamnatin Senegal ta katse sadarwar yanar gizo a fadin kasar a karo na biyu cikin wata guda tare da haramta zanga-zangar adawa da jinkirin zaben shugaban kasa da aka shirya yi a watan Febrairu.

https://p.dw.com/p/4cMhe
Zanga-zanga a Senegal
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Matakin da hukumomin Dakar din suka dauka na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa game da tashe-tashen hankula a kasar.

Akalla mutane uku sun mutu wasu sun jikkata a zanga-zangar da ta yi kamari bayan matakin Shugaba Macky Sall na dage lokacin zaben da aka tsara ranar 25 ga watan Fabrairu, wannan na cikin rikicin da Senegal ta shiga mafi muni cikin shekaru da dama.

Kungiyoyin ECOWAS da Tarayyar Turai da kuam Amirka, sun bukaci gwamnatin Macky Sall ta mutunta ainihin ranar gudanar da zaben shugaban kasa, sai dai gwamnatin Dakar ta ce matakin da ta dauka shi ne mafi a a la wa kasar don kauce wa kitso da kwarkwata bayan zabe.