1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: An yi wa 'yan tawaye afuwa

Abdourahamane Hassane
April 5, 2023

Ma'aikatar shari'a ta kasar Chadi ta sanar da cewar, an sako wasu gungun 'yan tawaye 380 da aka yi wa afuwa kwanan nan daga hukuncin daurin rai-da-rai,

https://p.dw.com/p/4PkOx
Tschad Armee FACT Rebellen Gefangene
Hoto: Chadian Army/AFP

'Yan tawayen na kungiyar FACT wadanda ake zargi da kisan Idriss Deby Into a shekara ta 2021, su dukkaninsu an yi musu afuwa,sai jagoran kungiyar Mahamat Mahdi Ali, da wasu mutanen 55 da aka yankewa hukunci ba a kan idanusu ba, wadanda ke yin gudun hijira. A cikin watan  Afrilu shekara ta 2021, yan tawayen  FACT sun ƙaddamar da farmaki zuwa N'Djamena daga sansaninsu a Libya.Kafin kashe garii rundunar sojin kasar Chadin ta sanar da cewa Marshal Idriss Deby ya rasa ransa a fagen dagga a fada da 'yan tawaye.